Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s}-abna-ofishin fatawa na Ayatullahi Sayyid Ali Khamna’I ya tabbatar da yau Alhamis ne daya ga watan Ramalana.
Sanarwar tazo a karshen daren jiya inda ofishin ya bada tabbaci da ingancin ganin watan , kuma ofisoshi goma na wasu marja’oin suma sun tabbatar da ingancin ganin watan saboda haka yau Alhamis ne suka sanar ta tazamo daya ga watan Ramalana.
Sauran ofisoshin da suka sanar sun hada da Ayatullahi Gholpygani, Ayatullahi Makarim shirazi, Ayatullahi Noori Hamdani, Ayatullahi Musawi Ardabili, Ayatullahi Sayyid Ha’iri, Ayatullahi Shahrudi, daga kuma marja’oin Iraki akwai Ayatullahi Hakim, da Ayatullahi Faiyaz, da kuma Ayatullahi Bashir Najafi.288